Daga Abdullahi dan Amr dan Al-Aas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai cewa Allah zai tseratar da wani mutum daga al'ummata agaban halittu a ranar Alkiyama, sai Ya bude masa fayil dinsa x asa'in da tara, kowanne fayil tamkar iya ganinka ne, sannan Ya ce: Shin kana musun wani abu daga wannan? Shin marubutaNa masu kiyayewa sun zalinceka ne? Sai ya ce: A'a ya Ubangiji, sai Ya ce: Shin kana da wani hanzari? Sai ya ce: A'a ya Ubangiji, sai (Ubangiji) Ya ce: Eh, lallai kanada wani abu kyakkyawa a wurinmu, a yau babu wani zalinci akanka, sai a fitar da wani kati a cikinsa akwai: Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah , kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, sai ya ce: ka zo wajan ma'aninka, sai ya ce; ya Ubangiji wannan wanne katine tare da wadannan fayilillikan? Sai Ya ce; Lallai cewa kai ba za’a zalinceka ba, sai ya ce: Sai a dora fayilillikan a bangaren ma'auni , katin kuma a daya ma'aunin, sai fayililliakn su yi sauki, kuma katin ya yi nauyi, wani abu ba zai yi nauyi tare da sunan Allah ba". Ingantacce ne - Tirmizi ne ya Rawaito shi
explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Allah Zai zabi wani mutum daga al'ummarsa agaban halittu , za'a kira shi dan a yi masa hisabi, sai (Ubangiji) ya bijiro masa da fayilillika casa'in da tara, su ne takardun ayyukansa wadanda ya kasance yana aikatasu a duniya, kuma tsawon kowane fayil tamkar iya ganinnka ne. Sannan Allah - mai girma da daukaka - ya cewa wannan mutumin: Shin kana musun wani abu daga abinda aka rubuta a cikin wadanannan fayilillikan? Shin Mala'ikuna masu kiyayewa masu rubutu sun zalinceka?. Sai mutumin ya ce: A'a ya Ubangiji. Sai Allah - mai girma da daukaka - ya ce: Shin kana da wani hanzari da za'a yi maka uzuri da shi daga abinda ka gabatar na ayyuka a duniya? daga kasancewarsa rafkanuwa ne, ko kuskurene ko jahilcine, Sai mutumin ya ce: A'a ya Ubangiji ba ni da wani hanzari. Sai Allah - mai girma da daukaka - ya ce: Eh, lallai kana da wani kyakkyawan aiki a wurinMu, kuma cewa babu wani zalinci akanka a yau. Ya ce: Sai a fitar da wani kati an rubutawa a ciki: Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina shaida cewa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne. Sai Allah - mai girma da daukaka - ya cewa wannan mutumin: ka zo wurin ma’aunin ka. Sai mutumin ya ce, yana mai mamaki; Ya Ubangiji! Menene nauyin wannan katin tare da wadannan fayilill din ??. Sai Allah - mai girma da daukaka - ya ce: Wani zalinci ba zai afku akanka ba. Sai ya ce ; sai a dora fayilillikan a ma'aunin, katin ma a daya ma'aunin; sai ma'aunin da fayilillkan suke a ciki su yi sauki, sai ma'aunin da katin yake ciki ya rinjaya, kuma ya yi nauyi, sai Allah Ya gafarta masa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Girman kalmar Tauhidi: Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, da nauyinta a ma'auni.
  • Fadin: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah ba ya isa da harshe kadai, babu makawa sai an san ma'anarta da kuma aiki da abinda take hukuntawa take nema.
  • Ikhlasi da karfin Tauhidi sababi ne na kankare zunubai.
  • Imani yana fifita da fififtar abinda ke cikin zukata na Ikhlasi, wani daga mutane zai iya fadin wannan kalmar saidai za'a yi masa azaba da gwargwadan zunubansa.