Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayyana hakkin Allah akan bayi, da hakkin bayi ga Allah, lallai cewa hakkin Allah akan bayi su bauta maSa Shi kadai kada su hada shi da wani abu. Kuma cewa hakkin bayi ga Allah shi ne ba zai azabtar da masu kadaitaShi da bauta ba, wadanda ba sa sanya masa abokin tarayya ba. Sannan cewa Mu'az, ya ce: Ya Manzon Allah, shin baa a yi wa mutane albishir da shi ba dan su yi farinciki, kuma su yi murna da wannan falalar ba ?? Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana shi dan tsoron kada su dogara akanta.