Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi nauyin abinda ke ma'aunin mumini ranar Alkiyama na ayyuka da maganganu shi ne kyawawan dabi'u, hakan ta hanyar sakin fuska, da barin cutarwa, da yin alheri. Allah - Madaukakin sarki - Yana kin mai munanawa a aikinsa da maganarsa, mai munanawa a abinda harshensa yake furtawa da shi.