Mummunar magana ko mummunan aiki ba su kasance cikin dabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ba, bai nufe shi ba, kuma bai ganganta yinsa ba, to, shi fa [Annabi] tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ma’abocin ɗabi’u ne masu girma. Kuma [Annabi] tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana cewa: Lalle mafi falalarku a wurin Allah mafi kyawunku kyawawan ɗabi’u, ta hanyar bayar da abu mai kyau, da sakin fuska, da kamewa daga cutarwa, da juriya, da hulɗa da mutane da abu mai kyau.