explain-icon

Bayani

Ɗaya daga cikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - ya nemi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya shiryar da shi a kan wani abin da zai amfaneshi, sai ya umarceshi da kada ya yi fushi, ma'anar hakan cewa shi ne ya nisanci sabubban da za su sa shi fushi, kuma ya tsare kansa idan fushi ya faru gareshi, kada ya zarce tare da fushinsa da kisa ko duka ko zagi da makamancin hakan. Mutumin ya maimaita neman wasiyya da yawa, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi bai ƙara komai a wasiyyarsa ba a kan "Kada ka yi fushi".

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Gargaɗi akan fushi da sabubbansa, domin cewa shine matattarar sharri, kiyayarsa shi ne matattarar alheri.
  • Yin fushi saboda Allah; kamar fushi a lokacin keta alfarmomin Allah ya na daga fushi abin yabo.
  • Maimaita zance a lokacin buƙata har mai ji ya kiyayeshi ya riski muhimmancinsa.
  • Falalar neman wasiyya daga malami.