wasu mutane biyu sun yi zage-zage a gaban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, alhali fuskar ɗayansu ta yi jā, jijiyoyinsa da suka kewaye wuyansa sun kunbura. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai ni na san kalmar da wannan mai fushin zai faɗeta da fushin ya tafi daga gare shi, da zai ce: Ina neman tsarin Allah daga Shaiɗan abin jefewa. Sai suka ce masa: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Ka nemi tsarin Allah daga Shaiɗan. Sai ya ce: Shin ni mahaukaci ne? ya yi zatan cewa ba mai neman tsari daga Shaiɗan sai wanda yake da hauka.