explain-icon

Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana cewa Allah mabuwayi Yana son wasu daga cikin bayinsa. Daga cikinsu akwai: Mai tsoron Allah wanda yake aikata abin da aka yi umarni, yake kuma nisantar hani. Kuma yana son: Wanda ya wadatu ga barin mutane, ya yi riƙo da Allah maɗaukaki, ba ya waigawa ga wanin Allah. Kuma yana son: Mai ɓoye kansa (wanda ba ya neman suna), mai tawalu’u, mai bauta ga Ubangijinsa, wanda ya shagaltu da abin da zai amfane shi, wanda bai damu da wani ya sanshi ba, ko wani ya yabe shi ba, ko ya burge ba.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Bayanin wasu siffofi masu sanyawa a samu son Allah ga bayinsa, wadanda suke su ne, Taƙ'wa da Tawalu’u da kuma yarda da abin da Allah ya raba.