Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiga masallaci, sai wani mutum ya shigo a bayansa sai ya yi sallah raka'a biyu da gaggawa, bai nutsu a cikin tsayuwarsa da ruku'unsa da sujjadarsa ba, Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana lura da shi a cikin sallarsa, sai ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a lokacin Ma’aikin Allah yana zaune a gefen masallaci sai ya yi masa sallama, sai ya amsa masa sallamar, kuma ya ce masa: Ka koma ka sake sallarka, domin kai baka yi sallah ba. Sai ya dawo yana sallah da gaggawa kamar yadda ya yi sallar, sannan ya zo sai ya yi sallama ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce masa: Ka koma ka yi sallah; domin kai baka yi sallah ba, ya aikata haka sau uku. Sai mutumin ya ce: Na rantse da wanda Ya aikoka da gaskiya, ba zan iya yin wacce tafi wannan ba to ka koya mini, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Idan ka tashi zuwa sallah to ka yi kabbarar harama, sannan ka karanta Fatiha da kuma abinda Allah Ya so ka karanta, sannan ka yi ruku'u har sai ka natsu kana mai ruku'u, shi ne ka sanya tafukanka biyu akan gwiwoyinka sai ka miƙar da bayanka ka tabbata dan yin ruku'inka, sannan ka ɗago ka daidaita bayanka har sai ƙasusuwa sun koma mararrabarsu kuma ka daidaita a tsaye, sannan ka yi sujjada har sai ka natsu kana mai sujjada, shi ne ka tabbatar da goshi tare da hanci, da hannaye da gwiwoyi da geffan diga-digai akan ƙasa, sannan ka ɗago har sai ka natsu kana zaune tsakanin sujjada biyu, sannan ka aikata hakan a kowace raka'a ta sallarka.