Abu kilabata yana cewa: Daya daga cikin sahabbai da ake kira maliku dan Huwairis ya zo masallacin mu, sai ya ce: lallai ni na zo wajenku don kawai nayi muku sallah domin na koyar da ku yadda sallar Annabi mai tsira da aminchi su kara tabbata a gareshi take a aikace, don koyarwar ta zamo a surar aiki zaifi zama mafi kusa kuma mafi wanzuwa a cikin kwakwalwar ku. sai marawaicin hadisin ya fada daga Abikilaba: yaya maliku dan Huwairis wannan da ya koyar da ku sallar annabi mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi ya kasance yana yin sallah? sai ya ce: irin sallar malamin mu Abi yazid shi ne Amru da salamata aljarmiy,ya kasance yana zama sassaukan zama yayi da ya dago kansa daga sujjada don mikewa tsaye, kafin ya tashi tsaye.