Wanna Hadisin yana bayanin Halaccin Al0qunuti a faruwar Wata Musiba, kuma cewa ita tana kasancewa ne bayan Ruku'u saboda aikin Manzon Allah SAW lokacin da banu sulaim suka warware masa Al-qawarin da ke tsakaninsu da Musulmai da kshe Mutum saba'in ko Arba'in na Makaranta Qur'ani waxan da Manzon Allah SAW ya turasu zuwa gare su sai yayi Al-qunuti wata xaya akan su bayan Ruku'i.