Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin Dora hukunci na (shari'a) wanda yake lazimtar 'ya'yan Adam ne sai waɗannan ukun: Ƙaramin yaro har sai ya girma ya balaga. Da mahaukaci wato mara hankali har sai hankalinsa ya dawo gare shi . Da mai bacci har sai ya farka. Ɗora shari'a haƙiƙa an ɗauke musu ita, kuma aikata laifinsu ba'a rubuta musu, sai dai ana rubuta alheri ga yaro ƙarami banda mahaukaci da mai bacci; domin su suna cikin wadanda ibadarsu ba ta inganta ba daga gare shi saboda gushewar ji.