Abu Barzah -Allah ya yarda da shi- ya fadi lokutan Sallar Farilla, Sai ya fara da cewa shi Annabi SAW ya Kasance yana Sallar Azahar, lokacin da Rana ta Karkata daga daga tsakiyar Sama zuwa Yamma, kuma wannan shi ne farkon lokacinta, kuma yana Sallar La'asar, sannan daya daga Masallatan ya dawo gidan sa a mafi nisan wuri daga Madina kuma Rana bata gushe ba tana nan, wannan shi ne farkon lokacinta, amma Magriba Mai riwayar ya manta abunda ya zo cikinta, kuma Nassoshi sun nuna haka Ijma'in Malamai kan cewa farkon lokacin ta da faduwar Rana, kuma Manzon Allah ya Kasance yana son ya jinkirta Isha, Saboda lokacinta wanda ya fi shi ne a Sallaceta a karshen lokacinta Na Mukhtari, kuma ya Kasance yana kin ayi Bacci kafinta don tsoron ya jinkirta ta daga lokacinta Mukhtari ko ya rasa Jam'i, da kuma tsoron bacci ya cimmasa da kuma barin Sallar dare kuma yana kin yin Hira bayanta saboda tsoron makara ga barin Sallar Asuba, ko rasa Sallar jam'i, Kamar yadda yana tafiya bayan Sallar Asuba, a lokacin da Mutum yana iya gane waye yake zaune a gefensa, tare da cewa zai Karanta a cikin sallarsa Aya Sittin zuwa dari, daga cikin abunda ya ke nuna cewa shi yana Sallatarta da duku duku.