Umar Allah ya yarda da shi y zo wajen Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Ranar yakin Gwalalo bayan faduwar Rana yana la'antar kafiran Kuraishawa; saboda sun shagaltar da shi daga yin Sallar La'asar don bai sami yinta ba har Rana ta kusan faduwa, sai Annabi tsira da anminci ya rantse cewa shima bai yi sallar ba har yanzu -Annabi kuwa shi ne Mai gaskiya- Annabi ya yi haka ne don Umar ya sami nutsuwa game da lamarin da ya dame shi. Sannan sai ya mike ya yi alwalla Sahabbai ma suka yi alwalla, sai ya sallaci La'asar sannan ya sallaci Magariba.