Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda ya yi sallah a tufa ɗaya ya tsiraitar da kafaɗunsa abinda ke tsakanin kafaɗa da wuya ta inda kada, ya sarayar da wani abinda zai suturtasu; domin kafaɗu biyu duk da ba al'aura ba ne, to lallai suturtasu ya fi tabbata a ɓoye al'aura, kuma shi ne mafi kusanci zuwa girmama Allah - Maɗaukakin sarki - da girmamaShi a tsakiyar tsayuwa a gabanSa a cikin sallah.