explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa imani yana tsufa a cikin zuciyar musulmi kuma yana rauni kamar sabon tufafin da yake tsufa saboda tsawon amfani da shi. Saboda yankewa a ibada, ko aikata sabo da afkawa a cikin sha'awowi. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da cewa mu roki Allah - Madaukakin sarki - ya sabunta imaninmu, ta hanayar tsayuwa da wajibai da yawan zikiri da istigfari.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Kwadaitarwa akan rokon Allah tabbata da sabunta imani a cikin zuciya.
  • Imani fada ne da aikatawa da kudircewa, yana karuwa da biyayya, kuma yana raguwa da sabo.