Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani Annabin da Allah Ya aiko shi a wata al'umma kafin shi sai ya kasance yana da tsarkakakku da mataimaka da mayaka masu ikhlasi a cikin al'ummarsa, wadanda suka cancanci kalifanci a bayansa; suna riko da sunnarsa, kuma suna koyi da umarninsa, sannan wasu mutane zasu zo bayan wadancan magabata na garin wadanda babu alheri a cikinsu; suna fadin abinda ba sa aikatawa, kuma suna aikata abinda ba'a umartarsu; wanda ya yakesu da hannunsa to shi mumini ne, wanda ya yakesu da harshensa to shi muminin ne, wanda ya yakesu da zuciyarsa to shi mumini ne, kuma babu wani imani kwatankwacin kwayar komayya bayan hakan.