Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin halin munafiki kuma shi kamar akuya ce mai kaikawo, ba ta san wanne garke za ta bi ba na tumakai, Tana tafiya zuwa wannan garken wani lokaci, da kuma zuwa wani garken a wani lokacin daban, Su masu dimuwane tasakanin imani da kafirci, su ba sa tare da muminai a zahiri da badini, kuma su ba sa tare da kafirai a zahiri da badini, su dai zahirinsu suna tare da muminai, kuma badininsu suna cikin kokwanto da taraddudi, wani lokaci yana karkata zuwa ga wadannan, wani lokacin kuma zuwa ga wadannan.