Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: Shin kun san waye muflis? suka ce: Muflis a cikinmu wanda ba shi da dukiya ko kaya, sai ya ce: Lallai muflis daga al'ummata zai zo ranar lahira da ayyuka na gari na sallah da azumi da zakka. Kuma zai zo haƙiƙa ya zagi wannan, ya yi wa wannan ƙazafi a mutuncinsa, kuma ya ci dukiyar wannan ya yi musunta, kuma ya zubar da jinin wannan ya zalinci shi, ya daki wannan ya wulaƙantashi, sai a bawa wanda aka zalinta daga kyawawan ayyukansa, idan kyawawan ayyukan suka ƙare kafin ya biya abinda ke kansa na haƙƙoƙi da abubuwan da aka zalinta, sai a ɗauki zunuban wanda aka zalinta sai a sanya su a takardun azzalimin, sannan a watsa masa sai a jefa shi a cikin wuta inda babu wani kyakkyawan aiki da zai rage gare shi .