Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya siffanta sashin abinda ke cikin ranar alƙiyama, kuma mutane za'a tarasu bayan tashinsu daga ƙaburburansu dan yin hisabi, kuma cewa halinsu zasu zama marasa takalma, tsirara babu tufafi, marasa kaciya kamar ranar da iyayensu suka haifesu, yayin da Uwar muminai Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ji hakan sai ta ce tana mai mamaki: Ya Manzon Allah ! maza da mata baki ɗayansu sashinsu yana kallon sashi?! Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa: Sha'anin tsayuwar da taruwa bayan tashi daga mutuwa a cikinsa akwai tsorace-tsoracen da zai ɗauke hankalin mutane da idanuwansu daga kallan al'aurori.