Sahabbai sun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a wani dare sai ya dubi wata - daren goma sha hudu -, sai ya ce: Lallai muminai za su ga Ubanbijinsu a hakika da ido ba tare da wani rikici ba, kuma cewa su ba za su yi cunkoso ba, kuma wahala ba zata samesu ba ko tsanani a yayin ganinsa - Madaukakin sarki -. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Idan kuna da ikon yanke abubuwan da zasu hana ku sallar Asuba da sallar La'asar to ku aikata, ku zo da su (Sallolin) a cike a lokacinsu a cikin jama'a, domin cewa hakan yana daga sabubban gani zuwa fuskar Allah - Mai girma da daukaka -, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya karanta ayar: {Ka tsarkake da godiyar Ubangijinka kafin bullowar rana da kafin faduwarta}.