Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya umarci dukkan wanda ya aikata wani zalinci ga ɗan'uwansa musulmi a mutunci ne, ko dukiya, ko jini ya nemi wanda ya zalinta ya yafe masa tunda yana duniya, tun kafin ranar lahira ta zo, inda dinari ko dirhami ba za su yi amfani ba ga wanda ya baiwa wanda ya zalinta ba, dan ya fanshi kansa da shi ba; domin sakayya a wannan ranar da kyawawan ayyuka ne da kuma munana. Inda wanda aka zalinta zai kwasa daga kyawawan ayyukan azzalimin gwargwdan zalincinsa, idan azzalimin ba shi da wasu kyawawan ayyuka sai a labtawa azzalimin munanan ayyukan wanda aka zalinta gwargwadan zalincin da ya yi.