Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bada labarin cewa za'a kusanto wa halitta rana a yinin alƙiyama, har ta zama kamar mil ne daga kawunansu. Tabi'i Sulaim ɗan Amir ya ce: Na rantse da Allah ban san waɗanne mil ɗin ake nufi ba, shin faɗin ƙasa, ko kuma mil ɗin da akewa ido kwalli da shi? Ya ce: Sai su zama akan gwargwadan ayyukansu a gumi; daga cikinsu akwai wanda guminsa zai kai zuwa idanun sawunsa, daga cikinsu akwai wanda zai kai zuwa gwiwowinsa, daga cikinsu wanda zai kai zuwa kwankwasonsa da maɗaurin tazugensa, daga cikinsu akwai wanda guminsa zai kai zuwa bakinsa sai ya hana shi magana. Ya ce: Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya yi nuni da hannunsa zuwa bakinsa.