Lokacin da aya ta sauka: {Lallai wallahi za a tambayeku a wannan yinin game da ni'ima} wato: Za a tambayeku game da tsayuwa da godiyar abin da Allah Ya yi muku ni'ima da shi, sai Zubair ɗan Al-Awwam - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ya Manzon Allah, shin wacce ni'ima ce za a tambayemu game da ita?! ni'imomi biyu ne kaɗai, da ba za su kai a tambaya ba, dabino ne da ruwa fa! Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: Lallai tabbas za a tambayeku game da ni'ima tare da wannan yanayin da kuke ciki, ni'imomi ne guda biyu masu girma daga ni'imomin Allah - Maɗaukakin sarki -.