explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah - su tabbata agare shi - ya ba da labari cewa wanda ya saurarawa wanda ake bi bashi, ko ya sarayar masa daga bashinsa, to, sakamakonsa: shi ne Allah Zai inuwantar da shi ƙarƙashin al-Arshinsa a ranar Alƙiyama, wanda rana zata kusanto kawunan bayi a cikinta, kuma zafinta zai tsananta akansu. Babu wanda zai samu wata inuwa sai wanda Allah Ya inuwantar da shi.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Falalar saukakawa bayin Allah - Maɗaukakin sarki -, kuma hakan yana daga sabubban da suke tseratarwa daga tsorace-tsoracen ranar alƙiyama.
  • Sakamako yana kasancewa daga jinsin aiki.