Daga Mikdam dan Maadikarib - Allah Ya yarda da shi - ya ce : Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbbata agare shi - ya ce "Ku saurara, kada wani mutum Hadisi ya je masa daga gareni alhali shi yana kishingide akan mazauninsa sai ya ce: Tsakanin mu da ku littafin Allah, abinda muka samu na halal a cikinsa mu halattashi, abinda muka samu a cikinsa na haram mu haramtashi, kuma lallai abinda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya haramta to kamar abinda Allah Ya haramtane". Ingantacce ne - Abu Dawud da Tirmizi da Ibn Majah ne Suka Rawaito shi
explain-icon

Explanation

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agar shi - ya bada labarin cewa hakika wani lokaci ya kusa , wani sinfi na mutane zasu zamo acikinsa a zaune, dayansu yana kishingide akan shinfidarsa, Hadisi zai isar masa daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya ce: Abinda zai raba tsakaninmu da ku a cikin al'amura shi ne Alkur’ani Mai girma shi ya ishemu, abinda muka samu a cikinsa na halal mu yi aiki da shi, abinda muka samu a cikinsa na haram mu nisance shi. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa duk abinda ya haramtashi ko ya yi hani gareshi a cikin sunnarsa to shi a hukunci kamar abinda Allah Ya haramtashi ne a cikin littafinSa; domin cewa shi ne mai isarwa daga Ubangijinsa.

explain-icon

Benefits from the Hadith

  • Girmama sunna kamar yadda ake girmama Alkur’ani kuma a yi riko da ita.
  • Biyayya ga Manzo ita ce biyayya ga Allah, kuma saba masa shi ne sabawa Allah - Madaukakin sarki -.
  • Tabbatar da hujjar sunna da kuma raddi akan wanda ya watsar da sunnoni ko ya musanta ta.
  • Duk wanda ya bijirewa sunna ya yi da'awar takaituwa akan Alkur’ani to shi wanda ya bijire musu ne gaba dayansu, kuma makaryaci ne a cikin da'awar bin Alkur’ani .
  • Daga cikin hujjojin Annabcinsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bada labari game da wani abu da cewa zai faru a nan gaba, kuma ya faru kamar yadda ya bada labarin.