Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana karar halin bayinsa, cewa su suna yi masa karya a labari, suna ha'intarsa a amana, suna yin algus a mu'amala, suna saba masa a al'amari, shi kuma yana zaginsu yana dukansu dan ladabtar da su, sai ya tambaye shi game da halinsa ranar Alkiyama tare da su? sai tsira da aminci su tabbata agare shi ya ce: Za'a lissafa abinda suka ha'inceka suka saba maka suka yi maka karya, kuma za'a lissafta ukubarka garesu, idan gwargwadan ukubar ta yi daidai da laifukansu to ba ka da komai, kuma babu komai a kanka, idan kuma gwargwadan ukubarka garesu kasa da laifukansu ne, ya zama falala da kari gareka a lada, idan ukubarka garesu sama da laifukansu ne za’a yi maka ukuba, za'a karbi gwargwadan karin daga gareka za'a ba su, sai mutumin yadan yi nisa ya fara kuka muryarsa tana sama, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce masa: Shin ba ka karanta littafin Allah ba; {zamu sanya ma'auni na adalci ga ranar Alkiyama ba za’a zalinci wata rai wani abuba, idan ya kasance kwatankwacin kwayar komayya ne zamu zo da ita, mun isa zama masu hisabi] [Al-Anbiya;47], ba za’a zalinci wani mutum wani abu ba ranar Alkiyama, kuma ma'aunai za su zama a tsakanin mutane da adalci, sai mutumin ya ce: Wallahi ya manzon Allah, ban ji komai game da ni da su ba sama da na rabu dasu da barinsu, ina shaida maka cewa su 'ya'ya ne sabo da Allah gaba dayansu; dan tsoron hisabi da azaba.