(Sayyidina) Abubakar Siddiƙ - Allah Ya yarda da shi - yana bada labari: Cewa mutane suna karanta wannan ayar: {Yaku waɗanda suka yi imani ku lizimci kawunanku, wanda ya ɓata ba zai cutar daku ba idan kun shiriya} [al-Ma'ida: 105]. Suna fahimta daga ayar cewa ya wajaba ga mutum ya yi ƙoƙari ya gyara kansa kawai, kuma ɓatan wanda ya ɓata ba zai cutar da shi ba bayan hakan, kuma su ba’a nema daga gare su su yi umarni da kyakkyawa kuma su hana mummuna ba. Sai ya sanar da su cewa ita ayar ba haka take ba, cewa shi ya ji annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: Lallai mutane idan suka ga azzalimi ba su hana shi zalincin ba, kuma suna da iko akan hana shin, ya kusa Allah Ya game su baki ɗaya da uƙuba daga gareShi, mai aikata abin ƙin, da mai yin shiru bai hana ba.