Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya buga misali ga tsayayyu akan dokokin Allah, masu tsayawa akan umarnin Allah, masu horo da aikin alheri, masu hani daga abin ki, da misalin masu afkawa dokokin Allah masu barin kyakkyawan aiki, masu aikata abin ki, da tasirin hakan a nasarar zamantakewar jama'a, kamar kwatankwacin wasu mutanene da suka hau jirgin ruwa, sai suka yi kuri'a ga wanda zai zauna a saman jirgin ruwan da wanda zai zauna a kasansa, sai wasu suka samu samansa, wasunsu kuma kasansa, wadanda ke kasa idan sun so samun ruwa sai sun wuce ta wurin wadanda ke saman, sai wadanda ke kasa suka ce: Da a ce zamu tsaga wata tsaga a daidai wurin mu a kasa mu dinga samun ruwa daga gareshi, har ya zama bamu cutar da wanda ke samanmu ba, da a ce wadanda ke sama sun barsu su aikata hakan da jirgin ruwan ya nitse da su gaba daya, da a ce sun hanasu hakan da duk jama' biyun sun tsira.