Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa daga mafi girma da anfanin nau'ikan jihadi a tafarkin Allah - Madaukakin sarki - shi ne kalma ta adalci da gaskiya a wurin azzalumin sarki (shugaba); domin cewa shi aiki ne da alama ce ta horo da aikin alheri da hani daga mummuna, daidai ne ya kasance da fada ne ko rubutu ko aikatawa ko wanin hakan wanda maslaha zata tabbata da shi kuma barna ta tunkude barna.