Wani mutum ya tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da shi zuwa aikin da idan ya aikata shi Allah zai so shi kuma mutane ma zasu so shi, sai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Allah zai so ka idan ka bar mafifici a duniya, da abin da ba zai amfaneka a lahira ba, kuma ka bar abin da zai iya yi wuwa a cikinsa akwai cutarwa a Addinika, kuma mutane zasu so ka idan ka guji abinda ke hannunsu na duniya; domin su a ɗabi'arsu suna sonta, wanda kuwa ya yi gogayya da su a kanta zasuƙi shi, wanda ya bar musu ita zasu so shi.