Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargadar da wanda ya nemi ilimi dan yi wa malamai alfahari, da bayyanar da cewa ni malami ne irinku, ko dan su yi magana da jayayya da wawaye masu karancin hankali, ko a nemi ilimi dan a bijiro a majalisai, a gabatar da shi akan waninsa a cikinsu. Wanda ya aikata haka; to cewa shi ya cancanci wuta da riyarsa da rashin tsarkake niyyarsa a cikin neman ilimi saboda Allah.