Sarkin muminai Umar ɗan Khaɗɗab - Allah Ya yarda da shi - ya kasance a majalisarsa a tare da shi akwai wasu Jama’a daga cikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - sai ya ce da su: Waye a cikinku ya ji manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yake bayanin fitintinu? Wasu daga cikinsu suka ce: Mu mun ji shi yana bayanin fitintinu, sai Umar - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wataƙila kuna nufin ibtila'i da jarrabar mutum a cikin abinda ya keɓance shi; a matarsa da ɗansa saboda yawan soyayyarsa garesu, da kuma ƙwauransa a kansu, da shagaltarsa da su daga alkairai da yawa, ko dan sakacinsa da abinda yake lazimtarsa na tsayuwa da haƙƙoƙinsu da ladabtar da su da kuma koyar da su, haka nan fitinar mutum a maƙwabcinsa da makamancin haka, wataƙila kuna nufin hakan? Suka ce: Eh, ya ce: wadannan wasu fitintinu ne da suke hukunta hisabi, daga cikinsu akwai zunuban da ake kwaɗayin kankaresu da kyawawan ayyuka kamar sallah da azimi da sadaka. Saidai waye a cikinku ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bayanin fitintinu masu gamewa saboda tsananin girmansu da yawan yaɗuwarsu suna girgiza mutane kamar girgizar kumfar kogi? Sai mutanen suka yi shiru, sai Huzaifa ɗan Yaman - Allah Ya yarda da su - ya ce: Ni na ji shi, sai Umar - Allah Ya yarda da shi - ya yi farin ciki, kuma ya ce masa: Ya mamakin ilimin babanka da ya haifi irinka; Faɗi, Huzaifa ya ce: (Manzon Allah) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Fitintinu zasu bayyana zasu ɗanfaru ta hanyar bijirowa da gefen zuciyar mutum, kamar yadda shinfiɗar tabarma take ɗanfaruwa da gefen mai bacci a kanta, kuma tsananin ɗanfaruwar fitintinun da ita yana tasiri a cikin zuciya, kuma waɗannan fitintinun zasu dinga dawowa, fitina zata maimatu bayan wata, duk zuciyar data shiga cikinta, kuma ta so ta, ta cakuɗa da ita kamar cakuɗar abin sha da kuma shigarta; zata yi baƙin ɗigo a cikin zuciyarsa, kuma duk zuciyar da taƙi karɓar fitintinun za’a yi farin ɗigo a cikinta har zuciyoyi biyun su zama akan nau'i biyu: Akan farar zuciya dan tsananinta akan ƙulla imani, da kuma kuɓutarta daga ɓaci, kuma fitintinu basu danfara da ita ba, kuma ba su yi tasiri a cikinta ba kamar falalin dutse mulmulalle wanda wani abu bai makale a jikin shi ba, dan haka wata fitina ba zata cutar da ita ba , har sai ya gamu da Allah. Ɗaya zuciyar kuma ita ce zuciyar da launinta ya canza zuwa baƙi saboda fitintinu kamar karkatacciya ko juyayyar butar da ruwa ba ya zama a cikinta, to haka wannan zuciyar take wani alheri ko wata hikima ba ta damfare da ita, bata sanin wani abin alheri, kuma bata inkarin wani abin ƙi, sai abinda ta so kuma ranta ya so shi kawai. Huzaifa ya ce wa Umar: Lallai waɗannan fitintinun wani abu ba zai fita daga garesu a cikin rayuwarka ba, kuma tsakaninka da su akwai wata kullalliyar ƙofa ta kusa a karyata, Umar ya ce: Shin karyawa za’a yi karara? inama dai a ce a buɗeta wataƙila ta kasance a dawo da ita sai a kulleta, Huzaifa ya ce: A'a, kai, karyata za’a yi, kuma lallai wannan ƙofar wani mutum ne da za’a kashe ko ya mutu. Kuma abinda na ambace shi labari ne na gaskiya, kuma ba ya cikin littattafan ma'abota littafi biyu (Yahudawa da Nasara), kuma ba ijtihadi ne na wani ma'abocin wani ra'ayi ba, kai daga Hadisin Annabi ne - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.