Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa: Shin kuna son in baku labari ? In sanar da ku da mafificin ayyukanku, kuma mafi ɗaukakarsu, mafi ƙaruwarsu, mafi tsarkinsu, mafi tsaf-tsaf ɗinsu a wurin Allah Mamallaki - Mai girma da ɗaukaka -? kuma mafi ɗaukakarsu a cikin masaukanku a aljanna? kuma mafi alheri gareku daga sadaka da zinare da azirfa? Kuma mafi alheri a gareku daga ku haɗu da kafirai dan yaƙi, sai ku daki wuyansu, su daki wuyanku ? Sahabbai suka ce: Eh, muna son hakan. (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ambatan Allah - Maɗaukakin sarki - a dukkan lokuta da kuma dukkan siffofi da halaye.