Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Shin ba na nuna muku abin da Allah Ya ke shafe kurakurai da shi ba, kuma Yake ɗaukaka darajoji da shi?" Suka ce: Na'am, ya Manzon Allah, ya ce: "Cika alwala a lokutan da ake ƙi, da yawan takawa zuwa masallatai, da jiran sallah bayan sallah, wadannan su ne shi ne zaman dako". Ingantacce ne - Muslim ne ya rawaito shi
explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi sahabbansa shin suna son ya nuna musu wasu ayyukan da za su zama sababi a gafarta zunubai, da shafesu daga littatttafan (mala'iku) masu kiyayewa, da ɗaukakar darajoji a cikin aljanna? Sahabbai suka ce: Eh, muna son hakan. Ya ce: Na farko: Gamewa da cika alwala a wahala; kamar (lokacin) sanyi da ƙarancin ruwa, da raɗaɗin jiki, da ruwan zafi. Na biyu: Yawan takawa - shi ne abinda ke tsakanin diga-digai biyu - zuwa masallatai, ta nisan gida da Masallacin, da yawan maimaita zuwa Masallaci. Na uku: Jiran lokacin sallah, da ratayar zuciya ga sallar, da yin tanadi gareta, da zama gareta a cikin masallatai dan jiran jama'a, idan ya sallace ta to ya jira wata sallar ta gaba a nan inda ya yi sallah. Sannan tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana cewa waɗannan al'amuran su ne zaman dako na haƙiƙa; domin suna toshe hanyoyin Shaiɗan ga mutum, kuma suna rinjayar da son rai, kuma suna hana rai daga shiga waswasi, sai rundunar Allah su rinjayi rundunar Shaiɗan da su; Hakan shi ne jihadi mafi girma, sai suka zama a matsayin zaman dako a kafofin maƙiya.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Muhimmancin kiyayewa akan sallar jam’i a cikin masallaci, da himmantuwa da salloli, da rashin shagaltuwa daga barin su.
  • Kyakkyawan tsarin karantarwar annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - da kwaɗaitarwarsa ga sahabbansa ta inda ya fara su da lada mai girma ta hanyar tambaya, wannan wata hanya ce daga hanyoyin koyarwa.
  • Fa'idar bijiro da tambaya da amsa: Zance yana kama zuciya a tsarin hukuncin a boye kafin a bayyana.
  • (Imam) Nawawi - Allah Ya yi masa rahama - ya ce: Wadancan su ne zaman dako, wato: Zaman dako wanda aka kwaɗaitar a cikinsa, kuma asalin zaman dako tsare abu, kamar shi ya tsare ransa akan wannan ɗa'ar, an ce: Lallai cewa shi ne mafificin zaman dako kamar yadda aka ce: Jihadi jihadin rai, zai iya yiwuwa cewa shi ne zaman dako wanda ya sawwaƙa wanda zai yi wu, wato: Lallai cewa shi yana daga nau'o'in zaman dako.
  • An maimaita kalmar "Zaman dako" kuma an yi mata Ma'arifa da (Al) ta ta'arifi; hakan girmamawa ce ga sha'anin waɗannan ayyukan.