explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa dukkanin kyautatawa da amfani ga wasu na magana ne, ko na aiki yana zama sadaka, kuma a cikinsa akwai lada da sakamako.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Lallai sadaka ba ta taƙaituwa a abin da mutum yake fitar da shi daga dukiyarsa, kai, yana tattaro kowane alherin da mutum zai aikatashi, ko ya faɗeshi ya sadar da shi zuwa wasu.
  • A cikinsa akwai kwaɗaitarwa a kan yin aikin alheri da dukkanin abin da a cikinsa akwai amfani ga wasu.
  • Rashin wulaƙanta wani abu daga aikin alheri ko da ya zama ƙarami ne.