Idan bawa ya aikata abin da ake nema daga ubangijinsa wajen yi masa hidima, da yi masa da'a da kyautatawa da ba shi shawara da tsayawa kan hakkin Allah - Madaukaki - daga aikata abin da Allah ya wajabta a kansa da nisantar abin da ya hana shi, to, za a ba shi lada sau biyu a ranar tashin kiyama. Saboda an damka masa wasu lamura guda biyu: Na farko hakkin maigida ne, idan kuwa ya yi na maigidan nasa, to za a ba shi lada. Na biyu: ladar yin biyayya ga Ubangijinsa, don haka idan bawa ya yi biyayya ga Ubangijinsa, zai samu lada.