Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo Madina, mutane suka ganshi sai suka fuskanci inda yake suna gaggawa, daga waɗanda suka fuskanci inda yake Abdullahi ɗan Salam - Allah Ya yarda da shi - ya kasance daga Yahudawa, lokacin da ya ganshi sai ya san cewa fuskarsa ba fuskar maƙaryaci ba ce; dan abinda ya bayyana gare shi na haske da kyau da kwarjini na gaskiya. Ya kasance farkon abinda ya ji shi daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cewa shi ya kwaɗaitar da mutane akan ayyukan da zasu zama sababin shiga aljanna, daga cikinsu: Na farko: Yaɗa gaisuwa da bayyanar da ita da yawaita ta ga wanda ka sani da wanda ma baka sani ba. Na biyu: Ciyar da abinci ta hanyar sadaka da kyauta da tarbar baƙi. Na uku: Sadar da zumunci ga wanda zumunci ko kusanci ya ƙullu tsakaninka da su ta ɓangaren uba ko uwa. Na huɗu: Sallar nafila tsayuwar dare alhali mutane suna bacci.