Sahabi maigirma dan Abbas Allah ya yarda dasu ya bada labari cewa ya kwana a wajan Gwaggwonsa matar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, don yai tsinkayi da kansa yadda tsayuwar daren Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi take yayin da Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya tashi da daddare, sai dan Abbas ya tashi don yai salla tare dashi, sai ya zama a hagun Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi a matsayin mamu;saboda cewa dama ita tafi kuma itace wajan tsayuwar mamu daga liman in ya kasance shi kadai ne sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya ruko kansa, ya jawo shi ta bayansa,sai ya tsayar dashi a damansa