explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana bayyana cewa mafi kusancin lokacin da bawa yake kusanci ga Ubangijinsa shi ne alhalin yana mai sujjada; hakan ya kasance ne saboda mai sallah yana sanya mafi ɗaukakar abin da ke jikinsa a kan ƙasa cikin ƙanƙan da kai da ƙasƙantarwa ga Allah - Mai girma da ɗaukaka - alhali shi yana mai sujjada. Haƙiƙa (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya yi umarni da yawaita addu'a a sujjada, sai ƙanƙar da kai ga Allah ya haɗu da faɗa da aikatawa.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Biyayya tana ƙarawa bawa kusanci ga Allah - tsarki ya tabbatar masa Ya ɗaukaka -.
  • An so yawaita addu'a a sujjada; domin cewa ita tana daga wuraren amsawa.