explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana ba da labarin cewa waɗanda suke hukunci da adalci da gaskiya a tsakanin mutane waɗanda suke ƙarƙashin shugabancinsu da hukuncinsu da iyalansu, cewa su za su zauna a kan abubuwan zama maɗaukaka haƙiƙa an haliccesu daga haske, don girmamawa garesu a ranar al-ƙiyama. Waɗannan munbarorin suna daman Ubangiji Al-Rahman, kuma su duka hannayensa biyun na dama ne.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Falalar adalci da kwaɗaitarwa a kansa.
  • Adalci mai gamewa ne ya tattaro dukkanin shugabanci da hukunci a tsakanin mutane, har adalci a tsakanin ma'aurata da 'ya'ya da sauransu.
  • Bayanin matsayin masu adalci a ranar al-ƙiyama.
  • Banbance-banbancen matsayiyyikan ma'abota imani a ranar al-ƙiyama kowanne da gwargwadon aikinsa.
  • Salon kwaɗaitarwa yana daga salon kiran da zai kwaɗaitar da wanda ake kira a aikin ɗa'a.