Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda aka haramtawa sauƙi to ba'a datar da shi ba a cikin al'amuran addini dana duniya haka da cikin abinda yake tasarrufi a cikinsa ga kansa, da kuma abinda yake tasarrufi a cikinsa tare da waninsa, to haƙiƙa an hana masa alheri gabaɗayansa.