Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa aikin mamaci yana yankewa da rasuwarsa,, kyawawan ayyuka basa samunsa bayan mutuwnrsa sai a waɗannan ukun; dan kasancewarsa ya zama sababinsu: Na farko: Sadakar da ladanta yake gudana kuma yake dawwama, ba mai yankewa ba, kamar waƙafi, da gina masallatai, da haƙa rijiyoyi, da wanin hakan. Na biyu: Ilimin da mutane suke anfanuwa da shi, kamar wallafa littattafan ilimi, ko kamar ya koyar da wani mutum, sai wannan mutumin ya yaɗa wannan ilimin bayan mutuwarsa. Na uku: Ɗa na gari mumini da zai yi masa addu'a.