Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa addu'ar musulmi ga ɗan'uwansa musulmi a bayan idon wanda aka yi wa addu'ar abar karɓa ce; domin cewa hakan ya fi kai matuƙa a cikin ikhlasi, kuma lallai cewa a wajen kan mai addu'ar akwai wani Mala'ikan da aka wakilta, a duk lokacin da ya yi wa ɗan'uwansa addu'a ta alheri, sai Mala'ikan da aka wakilta gare shi ya ce; Amin, kaima (Allah Ya baka) kwatankwacin abinda ka roƙa.