Annabi - tsira da amincin Alah su tabbata agare shi - ya yi bayani alhali shi yana zantar da mutane falala biyu masu girma: Na farko: Wanda ya yi alwala sai ya kyautata alwalar ya cikata ta fuskar da aka sunnanta, kuma ya ba kowace gaɓa haƙƙinta na ruwa, sannan ya ce: Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad bawan Allah ne kuma ManzonSa ne; sai an buɗe masa ƙofofin aljanna takwas zai shiga ta wacce yake so. Na biyu: Wanda ya yi wannan alwalar cikakkiya, sannan ya tashi bayan alwalar ya yi sallah raka'a biyu; yana mai fuskantosu da zuciyarsa da ikhlasi da ƙanƙar da kai, ya ƙanƙar dakai da fuskarsa da dukkan gaɓɓan jikinsa saboda Allah, sai aljanna ta wajaba gare shi.