Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari cewa yana da wani tafki a ranar Alkiyama, tsawonsa tafiyar wata ne kuma fadinsama kamar haka ne. Kuma lallai cewa ruwansa ya fi nono tsananin fari. Kuma cewa kamshinsa mai dadi ne ya fi kamshin almiski. Kuma kofinansa tamkar taurarin sama ne a yawansu, Wanda ya sha daga tafkin da wadancan kofinan ba zai yi kishirwa ba har abada.