explain-icon

Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da ɗabi'u biyu a cikin mutane suna daga ayyukan kafirai, da kuma ɗabi'un Jahiliyya, su ne: Na farko: Sukar nasabobin mutane da tauyesu da yi musu girman kai. Na biyu: Ɗaga murya a lokacin masifa dan yin fushi akan ƙaddara, ko yaga tufafi saboda tsananin baƙin ciki.

explain-icon

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

  • Kwaɗaitarwa akan ƙanƙar da kai da rashin yi wa mutane girman kai.
  • Wajabcin haƙuri akan masifa da rashin fushi.
  • Waɗannan ayyukan suna daga kafirci ƙarami, wanda wani yanki na kafirci yake tare da shi, ba zai zama kafiri kafircin da yake fitarwa daga Musulunci ba har sai kafirci babba ya tabbata gare shi.
  • Hanawar Musulunci game da dukkan abinda yake kaiwa zuwa rabuwa tsakanin musulmai na sukar dangantaka da waninsa.