Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da sahabbai akan su yi aiki, kuma su ji tsoron Allah gwargwadan ikonsu, ba tare da zurfafawa ko Gazawa ba, kuma su nufi daidai da aikinsu ta hanyar ikhlasi ga Allah da bin sunna dan a karɓi aikinsu sai su zama sababi ga saukar rahama garesu. Sannan ya ba su labarin cewa wani mutum aikinsa kawai ba zai tseratar da shi ba; kai babu makawa daga rahamar Allah. Suka ce: Har kai Ya Manzon Allah aikinka ba zai tseratar da kai ba tare da girman darajarsa? Sai ya ce: Har ni, sai dai in Allah Ya suturtani da falalar rahamarSa.