Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya labarta cewa Allah idan Ya so bawanSa mumini; mai biyayya ga umarninSa mai nisantar hane-hanenSa sai Ya kira (Mala’ika) Jibril: Lallai cewa Allah - Maɗaukakin sarki - Yana son wane to ka so shi. Sai shugaban mala'iku (Mala’ika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi - ya so shi, sai Jibril yayi kira a cikin mala'ikun sama: Lallai cewa Ubangijinku Yana son wane to ku so shi, sai waɗanda ke sama su so shi, sannan a sanya masa karɓuwa a cikin zukatan muminai da soyayya da kuma karkata gare shi da kuma yarda da shi. Idan Allah Ya ki wani bawanSa sai Ya kira Jibril: Lallai cewa Ni ina ƙin wane to ka ƙi shi, sai (Mala’ika) Jibril ya ƙishi, sannan Jibril yayi kira a cikin waɗanda ke cikin sama: Lallai Ubangijinku Yana ƙin wane to ku ƙishi; sai su ƙishi, sannan a sanya masa baƙin jini da ƙiyayya a cikin zukatan muminai.