Wasu jama'a suka zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, lokacin da suka iso wurinsa sai suka fadi - suna masu yabonsa - wasu daga cikin kalmomin da tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ki su, sai suka ce ; "Kai ne shugabanmu", sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Shugaba (Shi ne) Allah" Cikakken shugabanci nasa ne akan halittarSa su bayinSa ne. Suka ce : Kai ne "Mafificinmu a fifiko" kuma mafi daukakarmu a daraja da daukaka. kuma kaine "Mafi girmanmu a kyauta" mafi yawaitawarmu a kyauta da daukaka da daraja. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nuna musu su fadi maganarsu ta al'ada kada su kallafawa kansu lafazai, kuma kada Shaidan ya Ja su zuwa wuce gona da iri da kanbawar da zata afkar cikin abinda aka haramta na shirka da hanyoyinta.