Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana tsoratarwa a kan cewa ci gaba da zalunci da laifuka da shirka da zaluntar mutane a haƙƙoƙinsu, to, lalle Allah maɗaukaki Yana saurarawa azzalumi ya jinkirta masa, ya tsawaita masa a rayuwarsa da dukiyarsa ba zai gaggauta masa uƙuba ba, to, idan bai tuba ba sai ya damƙe shi, kuma ba zai sake shi ba, ba kuma zai ƙyale shi ba sabo da yawan zaluncinsa. Sannan sai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya karanta: Kuma haka damƙar Ubangijinka take idan ya damƙi alƙaryu suna azzalumai, lalle damƙarsa mai raɗaɗi ce kuma mai tsanani ce.